Free account: track your progress — Sign up free

BECE Hausa Language 2022 Objective — Question 1

Question 1 of 120 from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2022 Objective paper, with the correct answer and a full explanation.

Advertisement

Karanta waɗannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye. Wasan kwaikwayo ya daɗe da samuwa a ƙasar Hausa, ana yinsa tun kafin bayyanar musulunci. Asali ana kiran wasan kwaikwayo da suna "Gauta". Shi kuma wasan Gauta iri biyu ne a ƙasar Hausa. Na farko shi ne irin wanda ake yi a fadar Sarakuna, irin na Zazzau da Daura da Kano da Katsina da Sakkwato da ƙauyuka irin Dankanjiba. Na biyu kuwa shi ne wanda samari ke shiryawa a dandali lokacin bikin kaka ko wani shagalin aure ko suna ko bikin buɗar daji da sauransu. Irin wannan wasan akan gudanar da shi a ƙauyuka. Wasan Gauta ya sha bamban da wasanni irin su; shanci da dambe da kokawa da langa. Wasan Gauta da ake shiryawa a fadar Sarki, yawanci ƙwaraƙwaran Sarki ne suke yinsa, inda kowace za ta zaɓi Hakimin da take so ta kwaikwayi halinsa ko maganarsa ko tafiyarsa ko takamarsa ko shigarsa. Shi kuwa wasan Gauta na samari, akan shirya shi a fage ko dandamali inda kowa da kowa ke taruwa a yi ta kallo ana shagali da nishaɗi. Samari za su shirya wasanni iri-iri. Suna kwaikwayon yadda alƙali ke yin shari'a, ko yadda ake bikin aure da sauransu. Ƙwaraƙwaran Sarki a labarin na

  • A. gimbiyoyi
  • B. jakadu
  • C. matan SarkiCorrect
  • D. sa-ɗaku
  • E. zabiyoyi

Explanation

Labarin ya ce ƙwaraƙwaran Sarki ne ke yin wasan a fada, wato matan Sarki.

Advertisement

Sign up free to unlock

  • Score tracking
  • Practice history
  • Saved questions
  • Progress dashboard
  • Personalized sessions
  • Weak-topic breakdown

…and/or go further with premium services and No Ads.