Free account: track your progress — Sign up free

BECE Hausa Language 2022 Objective Past Questions

All 120 questions from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2022 Objective paper, with the correct answer and a full explanation for each. Free, no signup needed.

Advertisement

Hausa Language 2022 Objective — Question 1

Karanta waɗannan labarai, sannan ka amsa tambayoyin da ke biye. Wasan kwaikwayo ya daɗe da samuwa a ƙasar Hausa, ana yinsa tun kafin bayyanar musulunci. Asali ana kiran wasan kwaikwayo da suna "Gauta". Shi kuma wasan Gauta iri biyu ne a ƙasar Hausa. Na farko shi ne irin wanda ake yi a fadar Sarakuna, irin na Zazzau da Daura da Kano da Katsina da Sakkwato da ƙauyuka irin Dankanjiba. Na biyu kuwa shi ne wanda samari ke shiryawa a dandali lokacin bikin kaka ko wani shagalin aure ko suna ko bikin buɗar daji da sauransu. Irin wannan wasan akan gudanar da shi a ƙauyuka. Wasan Gauta ya sha bamban da wasanni irin su; shanci da dambe da kokawa da langa. Wasan Gauta da ake shiryawa a fadar Sarki, yawanci ƙwaraƙwaran Sarki ne suke yinsa, inda kowace za ta zaɓi Hakimin da take so ta kwaikwayi halinsa ko maganarsa ko tafiyarsa ko takamarsa ko shigarsa. Shi kuwa wasan Gauta na samari, akan shirya shi a fage ko dandamali inda kowa da kowa ke taruwa a yi ta kallo ana shagali da nishaɗi. Samari za su shirya wasanni iri-iri. Suna kwaikwayon yadda alƙali ke yin shari'a, ko yadda ake bikin aure da sauransu. Ƙwaraƙwaran Sarki a labarin na

  • A. gimbiyoyi
  • B. jakadu
  • C. matan SarkiCorrect
  • D. sa-ɗaku
  • E. zabiyoyi

Explanation

Labarin ya ce ƙwaraƙwaran Sarki ne ke yin wasan a fada, wato matan Sarki.

Hausa Language 2022 Objective — Question 3

Ƙwaraƙwara kan kwaikwayi waɗannan halaye in ban da

  • A. magana
  • B. shari'aCorrect
  • C. shiga
  • D. tafiya
  • E. takama

Explanation

Ƙwaraƙwara suna kwaikwayon hali, magana, tafiya, takama da shiga; shari'a ta samari ce.

Hausa Language 2022 Objective — Question 5

Ware bare dangane da fadar Sarakuna da ake gudanar da wasan Gauta.

  • A. Dan kanjibaCorrect
  • B. Daura
  • C. Kano
  • D. Katsina
  • E. Zazzau

Explanation

Dankanjiba ƙauye ne; sauran duka biranen fadar Sarakuna ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 6

Sarauta hawa-hawa ce. Misali a sarautun gargajiya na Hausa, Sarki shi ne a gaba da kowa, shi ne shugaba mai mulki da iko a kan ƙasa baki ɗayanta. Daga shi sai Waziri ko Madaki da sauran mataimakansa na cikin gari da na ƙauyuka. Waɗannan mutane su ne Hakimai. A cikin gari akan sami Makama da Ciroma da Turaki, da Iya da sauransu. Sunayen irin waɗannan Hakimai sun bambanta a wurare daban-daban na ƙasar Hausa. A ƙauyuka kuwa, ana samun Hakimai da Dagatai waɗanda suke rike da yankunan ƙasa. Su kuma masu binsu Magaddai ne, da masu Unguwanni, ko Bulamai ko Barumomi, ko masu gari. Bayansu sai masu gida manya da ƙanana. Shi kuma mai gida gwargwadon jama'ar da ke ƙarƙashinsa shi ne gwargwadon mulkinsa a gidansa. Bayan waɗannan sarautu da aka zana, tsarin sarautar gargajiya na Hausa ba ya cika, dole sai an sami Liman da Alƙali da waɗansu dattawa masu ba da shawara. Liman da Alƙali da waɗannan dattawa, galibi su ke zaɓen sabon Sarki, idan bukata ta taso. Bulama daidai yake da

  • A. Alƙali
  • B. Hakimi
  • C. Mai UnguwaCorrect
  • D. Makama
  • E. Waziri

Explanation

Labarin ya ambaci "masu Unguwanni, ko Bulamai", wato suna da ma'ana ɗaya.

Hausa Language 2022 Objective — Question 8

Ware bare dangane da Sarki.

  • A. Mai iko
  • B. Mai mulki
  • C. Mai zaɓen SarkiCorrect
  • D. Shugaba
  • E. Yana gaba da kowa.

Explanation

Liman da Alƙali da dattawa ne ke zaɓen Sarki, ba Sarki ba.

Hausa Language 2022 Objective — Question 10

Ware bare dangane da masu bin Dagatai.

  • A. Magaddai
  • B. Masu Unguwanni
  • C. Bulamai
  • D. Barumomi
  • E. HakimaiCorrect

Explanation

Hakimai da Dagatai suna sama; Magaddai da Unguwanni da Bulamai da Barumomi su ne masu binsu.

Hausa Language 2022 Objective — Question 11

"Yadda kasuwar garinmu take". Ana buƙatar mai rubutun Insha'in ya yi

  • A. bayani
  • B. muhawara
  • C. rubutun wasiƙa
  • D. sharhi
  • E. siffantawaCorrect

Explanation

Rubuta yadda wuri yake siffantawa ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 12

Ware bare dangane da rubutun wasiƙa ga Shugaba.

  • A. Adireshin mai rubutu kawai.Correct
  • B. Adireshin Shugaba da mai rubutu.
  • C. Gaisuwa
  • D. Kan wasiƙa
  • E. Mai ladabi a gareka.

Explanation

Wasiƙa ta ladabi tana da adireshin Shugaba da na mai rubutu; "mai rubutu kawai" ba daidai ba ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 13

Ana sakin layi domin

  • A. bambanta Insha'in muhawara da wasiƙa.
  • B. kammalawa.
  • C. kawo bayani daki-daki.Correct
  • D. ƙawata rubutu.
  • E. rufe bayani.

Explanation

Kowane layi yana ɗauke da ƙaramin bayani guda ɗaya daki-daki.

Hausa Language 2022 Objective — Question 14

A rubutun Insha'i na muhawara, ana buƙatar

  • A. kare kaiCorrect
  • B. labari mai al'ajabi
  • C. labari mai tarihi
  • D. luguden kalmomi
  • E. zayyana hoton abu a zuciyar mai karatu.

Explanation

Muhawara tana buƙatar kare ra'ayi da hujjoji.

Hausa Language 2022 Objective — Question 15

Wanne ne daidai dangane da tsarin rubutun Insha'i?

  • A. Gabatarwa→Ginshiƙi→Kammalawa.Correct
  • B. Gabatarwa→Kammalawa→Ginshiƙi.
  • C. Ginshiƙi→Gabatarwa→Kammalawa.
  • D. Ginshiƙi→Kammalawa→Gabatarwa.
  • E. Kammalawa→Ginshiƙi→Gabatarwa.

Explanation

Insha'i yana farawa da gabatarwa, sannan ginshiƙi, sai kammalawa.

Hausa Language 2022 Objective — Question 17

'Hula da takalmi' misalai ne na suna

  • A. ɗan aikatau
  • B. gagara ƙirga
  • C. gama-gari
  • D. na yankaCorrect
  • E. tattarau

Explanation

Hula da takalmi abubuwa ne da ake ƙirgawa, wato suna na yanka.

Hausa Language 2022 Objective — Question 23

Duk waɗannan hanyar jam'insu ɗaya ce, in ban da

  • A. lambuCorrect
  • B. layi
  • C. rafi
  • D. tsauni
  • E. zaure

Explanation

Layi→layuka, rafi→rafuka, tsauni→tsaunuka, zaure→zauruka; lambu→lambuna.

Hausa Language 2022 Objective — Question 30

Fito da harɗaɗɗiyar jimla daga waɗannan.

  • A. Ɗalibai ne waɗannan yaran.
  • B. Ɗalibai sun ci abinci jiya.
  • C. Ɗalibai sun ci abinci.
  • D. Ɗalibai sun sayo littafi da alƙalami da tawada.Correct
  • E. Ɗalibai sun yi rubutu a cikin littafi.

Explanation

Jimlar D tana haɗa abubuwa da "da", don haka harɗaɗɗiya ce.

Hausa Language 2022 Objective — Question 32

'Shehu ya wanke motar.' Wace nau'in jimla ce wannan?

  • A. Harɗaɗɗiya
  • B. Korau
  • C. Sarƙaƙƙiya
  • D. SassauƙaCorrect
  • E. Tambayau

Explanation

Jimlar tana da aikatau guda ɗaya kuma ba ta da mahaɗi, don haka sassauƙa ce.

Hausa Language 2022 Objective — Question 34

'Yara sun faɗi shekaranjiya.' Kalmar da aka ja wa layi ______ ce.

  • A. aikatau
  • B. bayanauCorrect
  • C. sifa
  • D. suna
  • E. wakilin suna

Explanation

"Shekaranjiya" tana nuna lokacin aiki, wato bayanau.

Hausa Language 2022 Objective — Question 38

Ana amfani da -una wajen jam'in waɗannan in ban da

  • A. ɗaki
  • B. hula
  • C. rafiCorrect
  • D. rumfa
  • E. tulu

Explanation

Ɗaki→ɗakuna, hula→hulunna, rumfa→rumfuna, tulu→tuluna; rafi→rafuka.

Hausa Language 2022 Objective — Question 39

Wace jimla ake yi wa laƙabi da mai goyo?

  • A. Harɗaɗɗiya
  • B. SarƙaƙƙiyaCorrect
  • C. Sassauƙa
  • D. Tambayau
  • E. Umurtau

Explanation

Jimla sarƙaƙƙiya tana ɗauke da ƙaramar jimla a bayanta ("goyo").

Hausa Language 2022 Objective — Question 40

Harɗaɗɗiyar jimla ana gane ta ne ta hanyar amfani da

  • A. ɗafi
  • B. gaɓa
  • C. goyo
  • D. mahaɗiCorrect
  • E. saiwa

Explanation

Harɗaɗɗiyar jimla tana haɗa jimloli da mahaɗi (da, kuma, sannan).

Hausa Language 2022 Objective — Question 58

Rivers State Government.

  • A. Dokokin Jihar Rivers.
  • B. Gwamnan Jihar Rivers.
  • C. Gwamnatin Jihar Rivers.Correct
  • D. Ma'aikatan Jihar Rivers.
  • E. Majalisar Jihar Rivers.

Explanation

"Government" a Hausa gwamnati ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 61

A taƙaice adabin baka na nufin

  • A. azancin magana a rubuce.
  • B. dogaye da gajerun zantuka.
  • C. wasannin da ake yi da ka.
  • D. zantuka na hikima da ake yi da ka.Correct

Explanation

Adabin baka zantuka ne na hikima da ake furtawa da baki ba a rubuce ba.

Hausa Language 2022 Objective — Question 63

Adabin baka na samar da duk waɗannan, amma ban da

  • A. adana hikimomi da ɗabi'o'i.
  • B. bayyana tsarin zaman al'umma.
  • C. kiyaye nasarorin magabata.
  • D. koyar da hanyoyin naƙaltar harshe.
  • E. koyar da naƙaltar iya karatu da rubutu.Correct

Explanation

Karatu da rubutu ba aikin adabin baka ba ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 64

Wanne ne ya fita daban daga misalan wasan tashe?

  • A. A sha ruwan tsuntsaye.Correct
  • B. Danda dokin ƙara.
  • C. Ga Mairama ga Daudu.
  • D. Ka yi rawa kai malam.
  • E. Tsoho da gemu ya tsufa.

Explanation

Sauran misalan wasan tashe ne; wannan ba haka yake ba.

Hausa Language 2022 Objective — Question 67

Duk waɗannan sun jiɓanci almara in ban da

  • A. ƙagaggun labarai ne yawanci.
  • B. lallai abin da ya faru ne.Correct
  • C. tsarawa da hikima.
  • D. tunani da hankali.
  • E. wasa ƙwaƙwalwa wani lokaci.

Explanation

Almara ƙagaggen labari ne, ba abin da ya faru da gaske ba.

Hausa Language 2022 Objective — Question 73

Maganganun da yara suke yi ta hanyar saka wasu sautuka tsakanin gaɓoɓin kalma shi ake kira

  • A. baƙar magana
  • B. habaici
  • C. ƙarangiyaCorrect
  • D. zambo
  • E. zaurance

Explanation

Wannan yaren yara ne da ake kira ƙarangiya.

Hausa Language 2022 Objective — Question 75

'Maganganun da suka danganci ba'a, da ke gudana tsakanin wasu ƙabilu ko gari da gari' shi ne

  • A. barkwanci
  • B. habaici
  • C. kirari
  • D. zamboCorrect
  • E. zaurance

Explanation

Zambo shi ne ba'a tsakanin ƙabilu ko gari da gari.

Hausa Language 2022 Objective — Question 78

Birnin Alƙalawa da Tsuntsuwa misalai ne na garuruwan da ______ ya yi yaƙi.

  • A. Aliyara Sarkin Bindiga
  • B. GandokiCorrect
  • C. Garba Gagare
  • D. Sarkin Sudan
  • E. Shehu Ɗan Hodiyo

Explanation

A cikin littafin Gandoki, shi ne jarumin da ya yi yaƙi a waɗannan garuruwa.

Hausa Language 2022 Objective — Question 91

'Wasan da ake riƙe babban ɗan yatsa na ƙafa, kuma a tsaya a kan ƙata ɗaya' shi ne

  • A. Allan baku
  • B. ina aka saka
  • C. kangal-kangal
  • D. kulli kucciya
  • E. langaCorrect

Explanation

Langa wasa ne na tsayawa da ƙafa ɗaya.

Hausa Language 2022 Objective — Question 92

'Yara, yara... Uwum uwum? Me kuke ci? Gandan kare da romon jaki.' Wannan misalin kalmomin wasan ______ ne.

  • A. Allan baku
  • B. ina aka saka
  • C. kangal-kangal
  • D. kulli kucciyaCorrect
  • E. langa

Explanation

Wannan waƙar wasan kulli kucciya ce.

Hausa Language 2022 Objective — Question 94

Usana a wasan 'Sufeto Tuje' shi ne

  • A. babban ɗan ciniki da aka yi ma sata.Correct
  • B. ɗan gwangwani.
  • C. ɗan kasuwa.
  • D. wanda ya dawo fatauci daga ƙasashen waje.
  • E. wanda ya yi zamba a banki ya gudu.

Explanation

Usana ne ɗan ciniki da aka yi wa sata.

Hausa Language 2022 Objective — Question 98

Waƙar da aka je Samaru Zariya ziyara ita ce waƙar

  • A. Gidan Audu Baƙo Zu.Correct
  • B. Ƙidaya (sansan).
  • C. Mu Ci Da Ƙasarmu.
  • D. Shirin Tuƙi Hannun Dama.
  • E. Ta'aziyar Tafawa Ɓalewa da Sardauna.

Explanation

Waƙar Gidan Audu Baƙo Zu ita ce ta ziyarar Samaru.

Hausa Language 2022 Objective — Question 99

"Magananu Yakubu zan waiwaya, Da shi da Manjo Hassan fitilun duniya. Kowa da kowa da yana yi muku addu'a, Allah sa su san 'yancin ƙasar Nijeriya." Daga wace waƙa aka tsakuro waɗannan baitoci? Waƙar

  • A. Buɗe Kos A Tsohuwar Laburare.
  • B. Gidan Audu Baƙo Zu.
  • C. Ƙidaya (sansan).
  • D. Shirin Tuƙi Hannun Dama.Correct
  • E. Ta'aziyar Tafawa Ɓalewa da Sardauna.

Explanation

Baitocin suna yabon Gowon da Manjo Hassan a lokacin gwamnatin soja.

Hausa Language 2022 Objective — Question 102

Jami'an ______ su ne masu kula da shigowar kaya.

  • A. gidan kurkuku
  • B. kula da zamantakewar jama'a
  • C. kwastanCorrect
  • D. shige-da-fice
  • E. 'yan sanda

Explanation

Jami'an kwastan ne ke kula da kayan da ke shigowa ƙasa.

Hausa Language 2022 Objective — Question 105

Duk waɗannan na daga cikin muhimmancin ibada in ban da

  • A. aikata ayyuka nagari.
  • B. alfahari da sana'a.Correct
  • C. ƙarfafa imani.
  • D. kyautata mu'amala.
  • E. samun tarbiyya.

Explanation

Alfahari da sana'a ba na ibada ba ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 108

Waɗannan duk hanyoyi ne na jagoranci, in ban da

  • A. ci gaban al'umma.
  • B. gudanar da mulki.
  • C. neman kuɗi.Correct
  • D. tabbatar da adalci.
  • E. zaman lafiya.

Explanation

Jagoranci ba don neman kuɗi ba ne.

Hausa Language 2022 Objective — Question 112

'Dogaro da kai da samun abin masarufi', misalai ne na dabarun

  • A. kyautata tsaro
  • B. riƙon iyali
  • C. riƙon sana'aCorrect
  • D. shugabanci
  • E. zamantakewar al'umma.

Explanation

Dogaro da kai yana zuwa ta riƙon sana'a.

Hausa Language 2022 Objective — Question 116

Tsaro zai inganta ta amfani da waɗannan hanyoyi, in ka cire

  • A. abokai nagari
  • B. kawo sabon saloCorrect
  • C. sa fitilu a kan hanyoyi
  • D. sa ido ga baƙi
  • E. sirrin bayanan kai rahoto

Explanation

Kawo sabon salo ba hanyar tsaro ba ne.

Advertisement

Sign up free to unlock

  • Score tracking
  • Practice history
  • Saved questions
  • Progress dashboard
  • Personalized sessions
  • Weak-topic breakdown

…and/or go further with premium services and No Ads.