BECE Hausa Language 2022 Objective — Question 6
Question 6 of 120 from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2022 Objective paper, with the correct answer and a full explanation.
Advertisement
Sarauta hawa-hawa ce. Misali a sarautun gargajiya na Hausa, Sarki shi ne a gaba da kowa, shi ne shugaba mai mulki da iko a kan ƙasa baki ɗayanta. Daga shi sai Waziri ko Madaki da sauran mataimakansa na cikin gari da na ƙauyuka. Waɗannan mutane su ne Hakimai. A cikin gari akan sami Makama da Ciroma da Turaki, da Iya da sauransu. Sunayen irin waɗannan Hakimai sun bambanta a wurare daban-daban na ƙasar Hausa. A ƙauyuka kuwa, ana samun Hakimai da Dagatai waɗanda suke rike da yankunan ƙasa. Su kuma masu binsu Magaddai ne, da masu Unguwanni, ko Bulamai ko Barumomi, ko masu gari. Bayansu sai masu gida manya da ƙanana. Shi kuma mai gida gwargwadon jama'ar da ke ƙarƙashinsa shi ne gwargwadon mulkinsa a gidansa. Bayan waɗannan sarautu da aka zana, tsarin sarautar gargajiya na Hausa ba ya cika, dole sai an sami Liman da Alƙali da waɗansu dattawa masu ba da shawara. Liman da Alƙali da waɗannan dattawa, galibi su ke zaɓen sabon Sarki, idan bukata ta taso. Bulama daidai yake da
- A. Alƙali
- B. Hakimi
- C. Mai UnguwaCorrect
- D. Makama
- E. Waziri
Explanation
Labarin ya ambaci "masu Unguwanni, ko Bulamai", wato suna da ma'ana ɗaya.
Advertisement
Sign up free to unlock
- Score tracking
- Practice history
- Saved questions
- Progress dashboard
- Personalized sessions
- Weak-topic breakdown
…and/or go further with premium services and No Ads.