BECE Hausa Language 2023 Objective — Question 1
Question 1 of 120 from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2023 Objective paper, with the correct answer and a full explanation.
Advertisement
Yawancin rubuce-rubucen da Hausawa suka fara yi ta hanyar rubutun ajami, salonsu na Larabawa ne. Wato rubutun wake-wake don jan hankalin al'ummarsu, kan wasu harkoki na addini. Wannan salo kuwa na rubutun waka ya samo asali tun zamanin jahiliyya a k'asashen Larabawa. Shi kuma (rubutun boko) Hausawa sun fara amfani da shi bayan an bud'e makarantun boko ne, a farkon k'arni na ashirin a k'asar Hausa. Hausawa sun yi rubuce-rubuce na aikin fassara, da k'agaggun labarai da sauransu, ta amfani da rubutun boko tun lokacin da aka fara samun mutanen da suka gama karatun bokon. Muhimmin lokacin da aka sami littattafan karatu na k'agaggun labarai, shi ne lokacin da aka yi gasar rubuta labarai wadda Hukumar Talifi ta Gaskiya, da ke Zariya ta shirya. Kafin nan kuwa akwai wake-wake da aka rubuta kamar dai yadda aka ambata a baya. Wad'annan hanyoyin rubutu a takaice da su aka yi amfani aka sami rubutaccen adabi. Hukumar Talifi ta Gaskiya ta samar
- A. harkokin addini
- B. k'agaggun labaraiCorrect
- C. makarantun boko
- D. rubutun ajami
- E. rubutun boko
Explanation
A cikin labarin, Hukumar ta shirya gasar rubuta k'agaggun labarai.
Advertisement
Sign up free to unlock
- Score tracking
- Practice history
- Saved questions
- Progress dashboard
- Personalized sessions
- Weak-topic breakdown
…and/or go further with premium services and No Ads.