BECE Hausa Language 2023 Objective — Question 6
Question 6 of 120 from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2023 Objective paper, with the correct answer and a full explanation.
Advertisement
Kasuwa dai nan ne wurin harkar saye da sayarwa. Kusan kowane abin sayarwa yana da wurin da ake sayar da shi a cikin kasuwa. Misali akwai ma'auna wato wurin 'yan sayar da kayan amfanin gona kamar su dawa da gero da shinkafa da wake da gurguzu da sauransu. Haka kuma, akwai wurin sayar da iri na saiwoyi, kamar su rogo da doya da dankali da walahan da dai sauransu. Mahauta ma wurinsu daban. Haka kuma akwai masayar dabbobi. Wurin 'yan sayar da kayan haja ma daban yake, wato masu sayar da turamen zannuwa da riguna, kai har ma da d'inkakkun kaya. Sannan akwai wad'anda su kam, zagaya, kasuwar suke, suna talla. Muhimmai cikin wad'annan kuwa su ne dillalai wad'anda su sana'arsu ke nan sayar da kayan sawa da sauran kayan ado irin na mata da na maza, kamar su cinko da munduwa, da 'yan kunne da gyalulluka da ma d'inkakkun riguna. Ware bare dangane da kayan gona masu saiwoyi.
- A. Dankali
- B. Doya
- C. GurguzuCorrect
- D. Rogo
- E. Walahan
Explanation
Gurguzu ba iri na saiwoyi ba ne.
Advertisement
Sign up free to unlock
- Score tracking
- Practice history
- Saved questions
- Progress dashboard
- Personalized sessions
- Weak-topic breakdown
…and/or go further with premium services and No Ads.