BECE Hausa Language 2024 Objective — Question 6
Question 6 of 120 from the Basic Education Certificate Examination (Junior WAEC) (BECE) Hausa Language 2024 Objective paper, with the correct answer and a full explanation.
Advertisement
Sai babbansu yace, "Baku gani har wani kallon hadarin kaji yake yi mana? Kila yana wani d'an gani-gani ne garemu ko? Iliya kuwa lalle a kaikaice ba'a yake yi musu. Ya sunkuyar da kansa k'asa ya ce 'Haba samari, tsofai-tsofai da ni, gani-ganin me zan yi maku? Ba ni da komai sai 'yan fam talatin da ...' ... na riko don guzuri. Wannan d'amarar ta zinariya ce, da kuka gani duka duka kud'inta bai fi fam d'ari biyu ba. Rigata kuwa duk an yi mata faci ta tsufa kud'inta ba zai wuce fam ashirin ba. Takalma da hulata kud'insu da k'yar zai fi fam goma sha d'aya. Wad'annan likafun da kuke kallo tsohuwar azurfa ce, jauharin da aka lillik'a musu shi ke sa kuke ganinsu kamar wani abin k'warai, kud'in su fam dubu biyu ne kawai. Sirdi na, ko da yake na k'arfe ne, ba zai wuce fam metan ba. Dutsen nan da ke bisa kan doki na kuwa, kun dai san darajarsa ba shi da wani amfani sai don ya k'ara wa dokin gani idan dare ya yi. Dokin kuwa ba shi da wani amfani in ba wuri na ba. To me zai sa ku tare ni? Ni ba ni da komai, ina rok'on ku, ku k'yale ni na yi tafiyata." Bai lissafa darajar kud'in ______ ba.
- A. dutseCorrect
- B. d'amara
- C. hula
- D. riga
- E. takalma
Explanation
Ya lissafa d'amara, riga, hula da takalma, amma ba dutse ba.
Advertisement
Sign up free to unlock
- Score tracking
- Practice history
- Saved questions
- Progress dashboard
- Personalized sessions
- Weak-topic breakdown
…and/or go further with premium services and No Ads.